in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka na ci gaba da martaba manufar Sin daya tak a duniya, in ji Rex Tillerson
2018-02-09 11:04:50 cri

Ministan harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce kasar sa na ci gaba da martaba kudurin nan na kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Mr. Tillerson ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da dan majalissar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, inda suka zanta game da alakar kasashen su, da kuma batutuwa dake jawo hankulan sassan biyu.

A nasa bangare, Yang ya ce Sin ta fayyace dukkanin batutuwa masu nasaba da yankin Taiwan, tana kuma fatan Amurka za ta lura da muhimmancin da Sin din ke baiwa lamarin.

Mr. Yang ya kara da cewa, hadin gwiwa mai nagarta dake tsakanin sassan biyu ya dace da moriyar al'ummun su, da ma na duniya baki daya.

Ya ce, yana fatan Amurka za ta ci gaba da hada kai da Sin, ta yadda za su kai ga bunkasa ci gaban dangantakar su cikin dogon lokaci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China