A baya, daya daga cikin dalilan da suka sa Amurka ta kaddamar da yakin cinikayya kan wasu kasashe da dama shi ne, kayayyakin da suke shiga Amurka daga kasashen waje suna samun rangame daga gwamnati. Amma yanzu Amurka ta fara samar da kudin rangwame ga manoman kasarta da kan ta, matakin da ya kasance tamkar ta mari kanta.
Wannan mataki da shugaba Trump ya dauka ya sake tabbatar da kashedin da masana tattalin arziki suka yiwa fadar White House, cewa ba wanda zai ci nasara a yakin cinikayya, sai dai kawai kowa ya sha kaye.
Manazarta na ganin cewa, Amurka za ta ci gaba yin yakin cinikayya ne ta hanyar samar da kudin rangwame ga manomanta, abun da ya nuna cewa, na farko, Amurka na da "fuskoki biyu" wato rashin gaskiya da nuna fin karfi a harkokin kasuwancin duniya. Na biyu kuma abun da Amurka ta yi ba ma kawai ya haifar da abubuwa masu nasaba da rashin sanin tabbas mai yawa ga sauran kasashe ba ne, da yin illa ga tsarin cinikayya dake kunshe da bangarori daban-daban, har ma ya kawo babban rashin tsari a cikin kasar ita kanta. (Murtala Zhang)