in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in kasar Jamus ya ce akwai alamar tambaya game da yarjejeniyar Trump da Juncker
2018-07-30 10:10:42 cri
Shugaban sashen tsara dokoki na kwamitin harkokin wajen jam'iyyar adawa ta AfD a Jamus, kuma mamba a majalissar dokokin kasar Petr Bystron, ya ce yarjejeniyar da kasar Amurka ta cimma da kungiyar tarayyar Turai ta EU ba ta da nasaba da manufar cinikayya cikin 'yanci, illa dai kawai wani salo ne na kyautatawa Amurka.

Mr. Bystron wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce ko ma ta yaya aka kalli wannan yarjejeniya, akwai ayar tambaya game da manufar EU ta sayen iskar gas da waken soya daga Amurka.

Ya ce shugaba Trump, da shugaban hukumar zartaswa ta kungiyar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker, sun cimma wasu kudurori a ranar Laraba, wadanda suka shafi kaucewa tsunduma yakin cinikayya baki daya. Hakan kuwa ya hada da daukar matakin gudanar da aiki tare, ta yadda za a dakatar da duk wani haraji, da shingayen cinikayya, da dakatar da biyan kudaden tallafi a hajojin da ba su shafi na kere-keren ababen hawa ba.

Kaza lika an jingine barazanar da Trump ya yi, game da kakabawa motocin Turai da ake shiga da su Amurka takunkumi, yayin da ita kuma Turai ta alkawarta sayen iskar gas da waken soya daga Amurka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China