Kamar yadda sanarwar ta nuna, hukumar rundunar 'yan sanda masu dauke da makamai za ta kasance a matsayin wani sashe ne karkashin ikon CMC, kuma ba za ta ci gaba da kasancewa a karkashin gudanarwar majalisar koli ta kasar Sin ba.
Sanarwar ta ce, za'a kafa wani tsarin gudanarwa na hadin gwiwa tsakanin kwamitin tsakiya, da hukumomin gudanarwa na kananan yankuna da kuma jami'an 'yan sanda masu dauke da makamai.
Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai, da rundunar sojoji ta PLA, da kuma jami'an 'yan sanda masu dauke da makamai da su aiwatar da wannan sabon tsari domin tafiyar da al'amurran tsaron kasa yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)