Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jamiyyar kwaminis na kasar Sin (CPC), kana shugaban kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasar Sin (CMC), ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake ba da umarni a taron da kwamtin ya shirya.
Wannan shi ne karon farko da kwamitin ya shirya taron ganawa da dukkan rundunonin sojin kasar.
Shugaba Xi ya bukaci rundunonin sojin kasar da su aiwatar da manufofin dake kunshe cikin babban taron wakilan CPC karo na 19, da kuma tunanin CPC don gina kakkarfar rundunar sojin Sin a sabon zamani. (Ahmad)