in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya isa Jamus domin ziyarar aiki
2018-07-09 10:01:30 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya isa Jamus a jiya Lahadi, domin halartar zagaye na 5 na taron tuntuba tsakanin gwamnatocin kasar Sin da Jamus.

Li Keqiang, ya bayyana cewa, shi da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, wadda ta ziyarci kasar Sin a watan Mayun da ya gabata, na ziyartar kasashen juna cikin kasa da rabin shekara, tun bayan da sabbin gwamnatocin kasashen 2 suka kama aiki

Firaministan wanda ke ziyara a kasar a karo na 4, Ya ce wannan alama ce dake nuna kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma burinsu na bai daya na hadin kai.

Ya ce duk da sarkakiya da sauyin yanayin harkokin duiniya, ya kamata gwamnatocin kasashen biyu su yi amfani da tarukan da suke yi wajen cimma matsaya guda da zurfafa hadin gwiwarsu tare da neman samun ci gaba.

Yayin ziyarar da za ta kai shi zuwa gobe Talata, Li Keqiang zai gana da Angela Merkel, kuma shugabanni 2 za su shaida rattaba hannu kan wasu jerin daftarori tare da halartar taro kan hadin gwiwar fasahohi da tattalin arziki tsakanin Jamus da Sin da

Firaministan na Sin, zai kuma gana da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China