in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaben shugaban kasa a Zimbabwe
2018-07-30 20:17:51 cri

A yau ne al'ummar kasar Zimbabwe suka fara kada kuri'a a zaben shugaban kasar na farko tun bayan da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya yi murabas a watan Nuwamba.

Rahotanni na cewa, tun da misalin karfe 7 na safe agogon kasar ce aka fara kada kuri'a a galibin runfunan zaben dake mazabar Warren Park dake Harare, babban birnin kasar, ana kuma sa ran rufe tashoshin zabe da misalin karfe 7 na yamma.

An ga masu zabe sun yi dogayen layuka a wajen tashoshin zabe dake Warren Park. Wasu masu kada kuri'a sun bayyana cewa, sun shiga layi don da tsakar dare, sun ce suna son sabuwar gwamnatin ta samar musu da ayyukan yi, ta magance matsalar kudi da kasar take fuskanta, kana ta inganta harkokin kiwon lafiya.

Al'ummar Zimbabwe dai za su zabi shugaban kasa da 'yan majalisun dattawa da na wakilai. Shugaba Emmerson Mnangagwa yana fafatawa da 'yan takara 22, da kuma babban abokin hamayyarsa, shugaban matasa na jam'iyyar adawa ta MDC, Nelson Chamisa. Kimanin mutane miliyan 5.6 ne suka yi rijistar kada kuri'a a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China