in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi alkawarin tallafawa zaben Zimbabwe
2018-03-16 13:41:59 cri
Jami'in kula da shirin raya kasashe na MDD(UNDP) Achim Steiner dake ziyarar aiki a kasar Zimbabwe ya bayyana kudurin majalisar na ganin ta taimakawa kasar shirya zabuka cikin nasara da adalci.

Achim Sterner wanda ya shaidawa manema labarai hakan bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Zimbabwe Sibusiso Moyo, ya ce a shirye MDDr take ta taimakawa kokarin da kasar ke yi na ganin ta shirya zabukan cikin adalci da ma farfado da tattalin arzikin kasar.

Tuni da shirin na UNDP ya taimakawa hukumar zaben kasar(ZEC) wajen ganin ta yiwa masu zabe rijista ta hanyar amfani da na'ura, inda yanzu haka aka yiwa 'yan kasar miliyan 5.3 rijistar shiga zabukan kasar masu muhimmanci da za shirya bayan murabus din da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya yi a watan Nuwanban da ya gabata.

Wannan dai ita ce ziyarar farko da jami'in na MDD ya kai kasar, tun bayan karshen gwamnatin Mugabe. A ranar 21 ga watan Agustan wannan shekara ce ake saran za a gudanar da zabuka a kasar ta Zimbabwe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China