in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi tir da harin da aka kai wajen gangamin siyasa a Zimbabwe
2018-06-27 09:36:32 cri

Sudan ta yi tir da harin da aka kai kan gangamin siyasa a garin Bulawayo na Zimbabwe, tana mai bayyana shi a matsayin laifin take darajar dan Adam da 'yan uwantaka a tsakanin al'ummar Afrika.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar, ta kuma jajantawa gwamnati da al'ummar Zimbabwe tare da yi wa wadanda suka raunana fatan samun sauki cikin gaggawa.

Ma'aikatar ta kuma jadadda matsayin Sudan na adawa da duk wani nau'i na laifuka da hari kan mutanen da ba-su-ji-ba-ba-su-gani-ba.

A ranar Asabar da ta gabata ne shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya tsallake rijiya da baya, biyo bayan wani hari da aka kai kan gangamin siysasa, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 2 tare da raunata wasu da dama. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China