in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da ambaliyar ruwa ya halaka a jihar Katsina ta Najeriya ya karu zuwa 62
2018-07-24 09:40:02 cri

A jiya Litinin hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa, yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar mamakon ruwan sama da aka sheka a ranar 15 ga watan Yulin wanda ya haifar da ambaliyar ruwa a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar ya karu zuwa 62.

An sake gano karin gawarwaki a cikin burabuzan gine ginen da suka rushe a garin Jibia a yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da ayyukansu, gabanin haka an gano gawarwakin mutane 52 ne wadanda galibinsu mata ne da kananan yara, kamar yadda mai martaba sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman, ya tabbatar da hakan.

A cewar alkaluman da gwamnatin jihar ta fitar, sama da gidaje 500 ne ambaliyar ruwan ta rusa a wasu kauyuka 5 dake karamar hukumar Jibia a ranar 15 ga watan Yulin, lamarin da ya haifar da rasa matsugunai na mutane sama da 5,000.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ta ce, mutane 24 ne ruwan ya yi awon gaba da su zuwa wasu kauyuka biyu dake makwabtaka da jamhuriyar Nijer.

Gwamnan jihar Aminu Masari ya ce, bayan ruwan da aka sheka kamar da bakin kwarya, ruwan kogi dake yankin ya kwarara zuwa garin Jibia, inda ya haddasa ambaliyar ruwan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China