in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Uganda
2018-07-27 10:50:40 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya jaddada cewa, a shekarun baya baya nan, dangantakar dake tsakanin Sin da Uganda na bunkasa cikin sauri. Ya kamata kasashen biyu su kiyaye yin mu'amala a tsakanin manyan jami'ansu, da nuna goyon baya ga juna kan muhimman batutuwan dake shafar moriyarsu. Sin tana goyon bayan matakan da kasar Uganda ke dauka na raya tattalin arziki da kyautata rayuwar jama'a. Sin tana son gudanar da manyan ayyukan hadin gwiwa tare da kasar Uganda, da zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni don amfanawa jama'arsu.

A nasa bangare, shugaba Museveni ya bayyana cewa, kasar Uganda tana godiya ga kasar Sin kan gudummawar da ta dade tana samar mata, kana ta gamsuwa sosai da ci gaban hadin gwiwar dake tsakaninsu. Kasar Uganda tana fatan kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin yankin masana'antu, da ayyukan yau da kullum, samar da wutar lantarki da sauransu, kana tana maraba da kamfanonin Sin su zuba kari tare kuma da gudanar da ayyuka a kasar Uganda. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China