in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WTO ta yi hasashen koma bayan cinikayya a shekarar 2016
2016-09-28 09:53:33 cri

Kungiyar cinikayya ta duniya WTO ta bayyana a cikin wani rahoto da ta wallafa a jiya Talata cewa, za a fuskanci koma baya a harkokin cinikayyar kasa da kasa a wannan shekara fiye da yadda ake zato.

Rahotan kungiyar na baya-bayan ya nuna cewa, a wannan shekara da muke ciki ta 2016, za a samu bunkasar kaso 2.2 cikin 100 na alkaluman GDP a duniya, bayanan da ke nuna cewa, wannan shi ne lokacin da aka samu koma bayan cinikayya da kuma kayayyakin da ake fitarwa tun bayan da duniya ta shiga rikicin kudi a shekarar 2009.

Haka kuma rahoton ya ce, koma bayan cinikayyar ta haifar da raguwar kayayyakin da ake sayarwa a rubu'i na farko na shekara, kana kasa da yadda aka yi hasashen zai farfado a rubu'i na biyu na shekara.

Bayanan na nuna cewa, sakamakon ya yi tasiri a kasashe masu tasowa, kamar Brazil da kasar Sin, da kuma arewacin Amurka. Kasashen da ke shigo da kayayyaki fiye da sauran shiyyoyi a shekarar 2014-15, amma suka fuskanci koma baya tun wancan lokaci.

Sai dai kuma kungiyar WTO ta yi hasashen cewa, al'amura za su inganta a rubu'i na uku na shekarar 2016, amma ba kamar yadda aka saba ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China