in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da EU sun amince su sassauta tankiyar cinikayyar dake tsakaninsu
2018-07-26 15:51:15 cri

A jiya Laraba ne shugaba Donald Trump na Amurka da shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Turai Jean-Claude suka amince su sassauta takaddamar cinikayyar dake kunno kai a tsakaninsu, biyo bayan karin kudin fiton da Amurka ta sanya kan wasu hajoji da kasashen mambobin kungiyar ke shigarwa cikin Amurkar

Sai dai kuma sassan biyu sun gaza daidaitawa kan karin harajin da Amurlar ta sanya kan motoci da karafa da sanholon ta EU din take shigarwa cikin kasar ta Amurka.

Bugu da kari, Amurka da EU sun yi hannu riga game da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, da yarjejeniyar canjin yanayi da aka cimma a birnin Paris, da matsayin birnin Kudus da kudaden da aka kashewa kan harkar tsaro da sauran batutuwa. Sannan dangantakar Trump da kasar Rasha ita ma ta haifar da rashin amincewa a Turai.

A cikin wata sanarwar bayan ganawar sama da sa'a guda da shugabannin suka fitar, Trump ya ce, Amurka da Turai sun amince su yi aiki tare don daina sanyawa juna haraji, da cire duk wani shinge game da harkokin kudin fito, da yiwa juna rangwame kan kayayyakin da ba su shafi masana'antu ba.

Bangarorin biyu sun kuma lashi takwabin hada kai don sassauta duk wani shinge da kara yin cinikayya a harkokin samar da hidima, sinadarai, da magunguna, da kayayyakin kiwon lafiya, da waken soya, kana EU a nata bangare, za ta sayi waken soya da dama da manoman Amurka dake jihohin tsakiya maso yammacin kasar ke nomawa.

Trump ya ce, kungiyar tarayyar Turai ta kuma shirya shigo da karin iskar gas daga Amurka, a kokarin fadada hanyoyinta na samun makamashi. Haka kuma sassan biyu sun amince su rika tattaunawa don rage tankiyar cinikayya, da sassauta matakan dake kawo cikas, da rage makuden kudaden da ake kashewa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China