in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta bukaci Amurka da ta daina lahanta moriyar saura
2018-06-19 18:51:06 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya mai da martani ga zargin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi a Talatar nan, game da manufar gudanar da tattalin arziki da cinikayya ta gwamnatin kasar Sin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan Amurka za ta yi hangen nesa, ta daina lahanta moriyar sauran kasashe.

Geng Shuang ya kara da cewa, dole ne a yi nuni da cewa, zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin ba shi da dalili ko kadan, kuma makasudin yin haka shi ne boye makarkashiyarta ta ba da kariya ga cinikayyarta. Kana jami'in ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta son yakin cinikayya, amma ba ta jin tsoron hakan, haka kuma za ta ci gaba da daukan matakai domin kare moriyar kasar ta, da moriyar al'ummun kasar, tare kuma da kare habakar tattalin arzikin duniya, da tsarin cinikayya tsakanin sassa da dama. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China