in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Trump ta soke wasu manufofin tsohuwar gwamnatin Obama game da ilimi
2018-07-04 10:31:48 cri

Sashen lura da harkokin ilimi na gwamnatin shugaba Donald Trump na Amurka, ya sanar da soke wasu manufofin tsohuwar gwamnatin shugaba Obama, wadanda a cewar sashen ke da nufin baiwa sassan al'ummun kasar masu tushe daban daban, damar shiga makarantun hukuma ba tare da nuna wani banbanci ba.

Da yake karin haske game da hakan cikin wata sanarwar da aka fitar, sakataren sashen ilimin Betsy DeVos, ya ce babbar kotun kolin kasar ta tantance dukkanin kudurori da suka dace da kundin tsarin mulkin kasar. Kuma kudurorin da kotun ta tabbatar a rubuce, na kunshe da abubuwan da suke mafiya dacewa, da matakan warware wannan batu mai sarkakiya.

Cikin sanarwar, Mr. Betsy ya bayyana cewa, cikin takardun manufofin 7 da aka soke, har da wadda take kunshe da batun amfani da matsayin tushen dan kasa a cibiyoyin ilimin Amurka, wadda aka kaddamar a ranar 2 ga watan Disambar shekarar 2011.

Har ila yau sashen ya yi imanin cewa, kudurorin tsohuwar gwamnatin, sun fi maida hankali ga burin mahukunta, maimakon tanaje tanajen kundin tsarin mulkin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China