in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nada sabon jami'in UN-Habitat
2018-07-26 10:57:27 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya sanar da nada Victor Kisob 'dan asalin jamhuriyar Kamaru a matsayin mataimakin babban sakataren kuma mataimakin babban daraktan kula da shirin raya garuruwa na MDD wato (UN-Habitat).

Kisob zai maye gurbin Aisa Kirabo Kacyira ta kasar Rwanda da zarar ya kama aiki. A wannan sabon mukamin nasa, zai taimakawa sakatare janar din da kuma babbar daraktar shirin UN-Habitat Maimunah Mohd Sharif wajen tafiyar da dukkan al'amurra da kuma yin sauye sauye a hukumar.

Kisob ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a sashen kula da ma'aikata, da harkokin kasa da kasa, da tsare tsare, da harkokin ilmi da yin hadin gwiwa, wanda ya hada ayyukan MDDr a kasashen Somalia, Isra'ila, Palestinu, Zambia da Habasha.

A halin yanzu yana rike da matsayin daraktan sashen ilmi da raya ci gaban dan adam na ofishin kula da ma'aikata na MDD (OHRM) dake birnin New York, kuma yana rike da wannan matsayi ne tun a shekarar 2015.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China