in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya goyi bayan wakilin musamman na MDDr a Syria
2018-07-26 10:37:09 cri

A jiya Laraba kwamitin tsaron MDD ya nuna goyon bayansa ga wakilin musamman na MDD kan rikicin Syria, Staffan de Mistura, a taron tattaunawar sulhu kan rikicin Syria a birnin Sochi na kasar Rasha, kamar yadda shugaban kwamitin ya tabbatar da hakan.

Olof Skoog, jakadan kasar Sweden wanda kasarsa ta karbi bakuncin taron kwamitin sulhun MDD na watan Yuli ya fadawa 'yan jaridu cewa, mambobin kwamitin sulhun MDDr sun nuna cikakken goyon bayansu ga shugabancinsa domin samar da ingantaciyar hanyar tabbatar da warware rikicin Syrian.

Bayan wani taron ganawar sirri da kwamitin sulhun MDD ya gudanar tare da de Mistura, Skoog ya ce, mambobin kwamitin sun nanata cikakken goyon bayansu na yin amfani da hanyoyin siyasa wadanda MDD ta tsara don warware rikicin Syriar.

Kwamitin sulhun MDDr ya bukaci dukkan bangarorin Syria da su shiga tattaunawar da kyakkywar fata, da zuciya daya kuma ba tare da gindaya wasu sharruda ba tare da de Mistura game da batun kafa kwamitin da zai tsara kundin tsarin mulkin kasar, in ji jakadan na Sweden.

Mahalarta taruka daban daban da aka gudanar a Sochi karkashin yarjejeniyar da aka cimma ta birnin Astana, sun amince a kafa kwamitin shirya kundin tsarin mulkin kasar, wanda shi ne zai shirya sabon kundin tsarin mulkin kasar ta Syria mai fama da tashin hankali.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China