in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta auna nasarorin da aka samu a ajandar ci gaba ta 2030
2018-07-19 10:00:33 cri

Babban magatakadar MDD Antonio Guterres, ya ce an samu ci gaba a wasu sassa na ajandar wanzar da ci gaba ta nan da shekarar 2030, yayin da wasu sassa kuma ke fuskantar koma baya.

Da yake tsokaci yayin rufe taron koli na masu ruwa da tsaki game da auna nasarorin da aka cimma game da ajandar ta 2030 a jiya Laraba, Guterres ya ce an samu nasarori a fannin rage mace macen mata masu juna biyu, da yara kanana. Kaza lika an samu nasarori a bangaren samar da ilimin bai daya a matakin farko, da bunkasa samar da makamashin lantarki da makamantan su.

Sai dai kuma a daya hannun, babban magatakardar MDDr ya ce an samu koma baya, a fannonin da suke da cikakken muhimmanci, musamman idan an yi la'akari da alkawuran da aka yiwa al'ummar duniya, na tabbatar da an samar da moriyar bai daya ga dukkanin bil Adama.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China