in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sahle-Work Zewde: Hadin gwiwar MDD da AU ya zama dole
2018-07-19 10:04:58 cri

Wakiliyar MDD a kungiyar tarayyar Afirka ta AU, kuma shugabar ofishin UNOAU Sahle-Work Zewde, ta ce ya zama dole MDD da AU su yi hadin gwiwa da juna, domin shawo kan kalubalen tsaro mai sarkakiya da ake fuskanta a sassan nahiyar Afirka.

Sahle-Work Zewde, wadda ta bayyana hakan yayin taron kwamitin tsaron MDD da ya gudana a jiya Labara, ta ce yanayin da ake ciki game da bukatar inganta tsaro da wanzar da zaman lafiya a Afirka, na bukatar hadin kan MDD da kuma AU.

Ta ce kamar yadda babban magatakardar MDD ya bayyana, yayin da ya halarci taron kwamitin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU a birnin Addis Ababan kasar Habasha cikin makon da ya shude, kungiyar AU ita ce jigon duk wani kawance da MDD za ta shiga, na tabbatar da tsaro da ci gaba, tare da kare hakkokin bil Adama a Afirka.

Zewde ta kara da cewa, sassan biyu sun ware wasu muhimman sassa na samar da ci gaba, sun kuma fidda tsare tsare na cimma nasarar hakan, bisa salon hada karfi da karfe, da mutunta juna, tare da musayar dabarun cimma nasarar da aka sanya gaba.

Jami'ar ta yi wannan tsokaci ne yayin da take yiwa zaman kwamitin na tsaro fashin baki, game da rahoton karfafa hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar AU a fannonin wanzar da zaman lafiya da tsaro a Afirka, ciki hadda ayyukan ofishin MDDr na UNOAU.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China