in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres: Taron sassan kasar Syria ya karfafa min gwiwa
2017-02-24 15:17:25 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce haduwar tsadin gwamnati da na 'yan adawar kasar Syria a birnin Geneva, domin fara tattaunawa ya karfafa masa gwiwa, bisa kudurin da aka sanya gaba na kawo karshen rikicin siyasar kasar cikin lumana.

Wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, ta rawaito Mr. Guterres na cewa, bayan shekaru 6 ana dauki ba dadi, yanzu lokaci ya yi da sassan masu ruwa da tsaki a kasar ta Syria za su rungumi hanyar sulhu da zuciya daya.

Ya ce, duk da cewa ba abu ne mai sauki a kai ga cimma nasarar da ake fata ba, duk da haka al'ummar Syria ba ta da wata mafita, wadda ta wuce ta gudanar da shawarwari. Ya kuma yi fatan 'yan kasar da suka amince da hakan, za su kara himma wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da lumana.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China