in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon Sin ya yi kira a warware batun Syria ta hanyar siyasa
2017-03-01 10:34:14 cri

Jiya Talata zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana kokarin warware batun Syria, a saboda haka ya kamata a nace ga manufar warware batun ta hanyar gudanar da shawarwarin siyasa.

A jiyan ne kuma yayin zaman kwamitin sulhun MDD aka jefa kuri'u kan daftarin kuduri game da batun makaman guba na Syria, amma ba a zartas da kudurin ba. Daga baya, Liu Jieyi ya bayyana cewa, a kokarin da kasashen duniya suka yi, an cimma burin tsagaita bude wuta a cikin yankunan kasar ta Syria a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kana ana gudanar da sabon zagaye na shawarwarin zaman lafiya game da kasar ta Syria a birnin Geneva, ana iya cewa, an samu wasu sakamako a fannin, saboda haka, ya kamata a ci gaba da yin kokari matuka domin ganin bangarori daban daban dake cikin kasar sun ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu, ta yadda a karshe za su kai ga bullo da wata dabarar shimfida zaman lafiya a fadin kasar da dukkansu za su amince da ita.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China