in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD zai kada kuri'ar tura jami'an sa ido zuwa Aleppo na Syria
2016-12-19 09:19:42 cri

Wakiliyar Amurka a MDD Samantha Power, ta ce a yau Litinin ne kwamitin sulhu na majalisar, zai kada kuri'ar amincewa da wani kuduri dake da nufin tura jami'an sa ido zuwa Aleppo, domin duba yadda aikin kwashe mutane ke gudana a yankin da aka yiwa kawanya.

Samantha Power ta ce, sabon kudurin, na neman babban sakataren majalisar ya samu jami'an majalisar da dama da za su iya zuwa Aleppo, inda ta ce, ana sa ran yau da misalin karfe 9, dukkan 'yan majalisar su kada kuri'ar amincewa da wannan kuduri.

Da farko, a jiya Lahadi, kwamitin sulhun ya yi wata tattaunawar sirri, kan wasu kudure-kudure biyu da kasashen Rasha da Faransa suka aike da su majalisar, kan yadda za su samu damar bibiyar aikin kwashe mutanen, tare da tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula.

Kudurin na Faransa, na neman majalisar dinkin duniya ta tura jami'an sa ido Aleppo ba tare da bata lokaci ba, yayin da na Rasha, ke bukatar a nemi amincewar gwamnatin Syria kafin aikewa da jami'an.

Bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa kan kudure-kuduren, 'ya'yan kwamitin sun ce, sun samar da wani kuduri guda, inda za a kada kuri'a a kai yau da safe. ( Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China