in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wasanni na Uganda ya jinjinawa gudummawar Sin a fannin raya wasanni
2018-01-11 09:13:07 cri

Ministan ma'aikatar wasanni na kasar Uganda Charles Bakkabulindi, ya yabawa gudummawar da kasar Sin ke baiwa kasar sa, ta fuskar raya wasannin motsa jiki.

Bakkabulindi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, babban filin wasa na Mandela da kasar ta Sin ta taimaka wajen ginawa a Uganda, ya habaka fannin wasan kwallon kafa, da sauran wasannin motsa jiki a kasar.

Ya ce, filin wasan na da kayayyaki na zamani, kuma Uganda na cin gajiya daga gare shi, sakamakon ingancin dangantaka dake tsakanin ta da Sin.

Filin wasan dai na iya daukar mutane 45,500, kuma kasar Sin ce ta samar da tallafin dalar Amurka miliyan 36 domin gina shi.

Tun bude filin wasan a shekarar 1997, Uganda da Sin ke ci gaba da gudanar da yarjejeniyar lura da shi, ta yadda za a dade ana cin gajiyar kayayyakin da aka tanada a cikin sa.

Shi ma kwamishina mai lura da harkokin motsa jiki da wasanni a ma'aikatar ilimi da wasannin kasar ta Uganda Lamex Omara Apitta, ya yaba da yarjejeniyar shekaru 2 da aka kulla tsakanin Uganda da kasar Sin, game da lura da filin wasan na kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China