in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Museveni ya yaba da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Uganda
2017-09-26 09:45:04 cri

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya yaba da kyakkyawar alakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, yana mai cewa, kasar Sin ce ta dauki nauyin galibin aikin samar da kayayyakin more rayuwa da aka gudanar a kasarsa.

Shugaba Museveni wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a bikin da Sinawa mazauna Uganda suka shirya a jiya Litinin don murnar cika shekaru 68 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ya kuma yaba da manufofin kasar Sin na rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, ko gindaya wani shadari ko ta fada musu abin da za su yi yayin da suke kokarin raya kansu.

A nasa jawabin, jakadan kasar Sin dake Uganda Zheng Zhuqiang, ya yaba da irin goyon bayan da Uganda take baiwa kasar Sin a harkokin kasa da kasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China