in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu ya yi wa ministocinsa garambawul
2018-02-27 08:55:27 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya yi ministocinsa tankade da rairaya jiya da daddare, inda ya sallami wasu daga cikinsu tare da sauyawa wasu ma'aikatu.

Cyril Ramaphosa ya bayyana garambawul din ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiyan a Pretoria, inda ya ce, yayin aiwatar da sauyin, ya yi la'akari da bukatar dake akwai na daidaita ci gaba da kwanciyar hankali da farfado da tattalin arziki da gaggauta samar da sauye-sauye na ci gaba.

A yau Talata ne ake sa ran rantsar da sabbin ministocin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China