in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun Rwanda: Sin sahihiyar aminiya ce ga kasashen Afrika
2018-07-25 09:29:47 cri

Kwararrun kasar Rwanda sun bayyana a lokacin zantawarsu da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasar Sin muhimmiyar kawa ce ga yawancin kasashen Afrika.

Ismael Buchanan, shugaban kwalejin nazarin tattalin arziki ta jami'ar Rwanda ya ce, kasar Sin da kasar Rwanda suna da kyakkyawar alaka mai dadadden tarihi, kuma ana samun kyakkyawan sakamako na hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni da dama da suka hada da bangaren cinikayya, kiwon lafiya, ilmi, yawon shakatawa, samar da kayayyakin more rayuwa.

Buchanan, wanda ya nuna gamsuwa da irin taimakon da kasar Sin ke baiwa Rwanda a cikin dogon lokaci, ya ce kasar Sin sahihiyar aminiya ce ga yawancin kasashen Afrika.

Ya bayyana cewa dangantakar dake tsakanin Sin da Rwanda, da kuma tsakanin Sin da Afrika an gina ta ne bisa ka'idojin mutunta juna da girmama juna, da inganta rayuwar al'ummomin sassan biyu da kuma samun bunkasuwa tare.

Eric Ndushabandi, daraktan cibiyar nazarin zaman lafiya da sasanto dake Kigali ya ce, kasar Sin tana kara zama babbar hanyar zuba jari a nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China