in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jack Ma zai halarci taron matasa 'yan kasuwa na Afirka a Rwanda
2017-06-12 09:14:11 cri

Hamshakin 'dan kasuwar nan 'dan kasar Sin, kuma jagoran kamfanin cinikayya ta yanar gizo na Alibaba Group Jack Ma, zai halarci taron matasa 'yan kasuwa da masu zuba jari a fannin sana'o'in zamani na Afirka da za a gudanar a binin Kigalin kasar Rwanda.

Za dai a gudanar da taron mai lakabin "YouthConnekt Africa Summit" ne tsakanin ranekun 19 zuwa 21 ga wata mai zuwa, kamar yadda ma'aikatar matasa da harkokin fasahar sadarwar kasar Rwanda ta bayyana.

Ana sa ran taron zai maida hankali ga nazartar damammaki da matasa ke da su wajen bunkasa sana'o'i a nahiyar Afirka.

Da yake karin bayani game da halartar Jack Ma, ministan ma'aikatar matasa da harkokin fasahar sadarwar kasar Rwanda Jean Philbert Nsengimana, ya ce suna ci gaba da tuntubar jagoran kamfanin na Alibaba Group, suna kuma da karfin gwiwar Mr. Jack din zai halarci taron kamar yadda aka tsara.

Ya ce, 'dan kasuwar na cikin masu gabatar da jawabai a yayin taron, baya ga shugaban kasar Rwandan Paul Kagame, da babban sakataren MDD mai lura da dandalin kasuwanci da ci gaba na UNCTAD Mukhisa Kituyi.

Sauran manyan baki yayin taron sun hada da Mr. Abdoulaye Mar Diye, daraktan shiyya na ofishin samar da ci gaba na MDD ko UNDP a takaice.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China