in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na da burin aiwatar da kudurorin da shugabanta ya cimma da takwaransa na Rwanda
2017-06-27 08:57:46 cri

Wakiliyar musamman ta kasar Sin game da kasashen Afirka Xu Jinghu, ta ce kasar ta, na fatan yin aiki kafada da kafada da kasar Rwanda, domin aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Xu Jinghu, wadda ke wannan tsokaci yayin ganawar ta da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ta ce tun kafuwar huldar diflomasiyyar kasashen biyu shekaru 46 da suka gabata, kawance tsakanin kasashen 2 ke ci gaba da bunkasa cikin kyakkyawan yanayi.

Jami'ar ta kara da cewa, yayin ziyarar da shugaban na Rwanda ya kai Sin cikin watan Maris, shi da mai masaukin sa shugaba Xi Jinping, sun cimma matsa kan wasu muhimman batutuwa, na ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen su gaba. Ciki hadda burin Sin na aiki tare da Rwanda a fannonin fadada kawance, da hadin gwiwa don cimma moriya a dukkanin fannoni, tare da daukar matakan kara inganta rayuwar al'ummun kasashen biyu, karkashin leman dadaddiyar alakar dake tsakanin su.

Xu Jinghu ta gudanar da ziyarar aiki ne a Rwanda tsakanin ranekun 24 zuwa 26 na watan Yunin nan da muke ciki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China