in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IFRC ta ce akwai sauran rina a kaba game da yakin da ake yi da Ebola a DRC
2018-05-23 10:52:43 cri

Darakta mai lura da nahiyar Afirka a hukumar ba da agajin jin kai ta kasa da kasa IFRC Dr. Fatoumata Nafo-Traore, ta ja hankalin masu ruwa da tsaki, game da muhimmancin ci gaba da ayyukan yaki da cutar Ebola a janhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, tana mai cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba game da wannan aiki.

Dr. Fatoumata Nafo-Traore ta ce, har yanzu masu aikin agaji na sanya ido, tare da karfafa lura game da yanayin da al'ummun kasar ke ciki. Hakan a cewar ta wani mataki ne na tabbatar da dakile yaduwar cutar zuwa kasashe makwafta.

Dr. Nafo-Traore, ta kara da cewa, daya daga cikin muhimman darussa da IFRC ta koya daga yaduwar cutar Ebola, shi ne gamsuwa da kananan matakai na iya haifar da gagarumin hadari.

Ta ce, yanzu haka IFRC ta kaddamar da asusun neman tallafi na gaggawa ga janhuriyar dimokaradiyyar Congo na kimanin dalar Amurka miliyan 1.6, domin taimakawa ayyukan hukumar Red Cross, wanda zai shafi 'yan kasar sama da mutane 716,000 cikin watanni 6 masu zuwa.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta bayyana cewa, an samu bullar sabbin wadanda suka kamu da cutar ta Ebola 51, ya zuwa Juma'ar da ta gabata a janhuriyar dimokaradiyyar Congo, ciki hadda 28 da aka tabbatar sun kamu, sai kuma 21 da ake kila wa kala game da kamuwar su, kana 2 kuma ba a kai ga tabbatar da matsayin su ba. Kaza lika adadin wadanda cutar ta hallaka sun kai mutane 27.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China