Rahotannin da aka ruwaito sun ce, ma'aikatar lafiya ta Jamhuriyar Demokuradiyyar Kango ta sanar da cewa, an dasa aya ga annobar Ebola wadda ta barke tun watan Mayun shekarar da muke ciki. Madam Hua ta ce, ba tare da wani jinkiri ba, kasar Sin ta bada kyautar tufafin kariya, da marufin hanci da baki, gami da safar hannu ga kasar Kango Kinshasa, ta kuma samar mata da tallafin jin-kai. Haka kuma, likitoci kwararru na kasar Sin sun je kasar Kango Kinshasa a farkon watan Yuni, don taimaka mata shawo kan yaduwar cutar Ebola.
Madam Hua ta jaddada cewa, matakan da kasar Sin ta dauka sun shaida irin dankon zumunci, da kyakkyawan hadin-gwiwa da dangantaka tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kango, har ma da duk nahiyar Afirka baki daya, abun da ya samu babban yabo daga gwamnatin kasar, gami da kasashen duniya daban-daban.
Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka wajen inganta kwarewarsu ta fuskar yaki da yaduwar cututtuka, da karfafa tsarin kiwon lafiyar jama'a.(Murtala Zhang)