in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba ta jin tsoron matakin Amurka na karbar harajin kayayyakin kasar ta
2018-07-23 19:33:36 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasarsa ba ta jin tsoron kalubalen da shugaban kasar Amurka ke haifarwa, game da karbar harajin kayayyakin cinikayya na Sin da ake shigarwa Amurka, wadanda suka kai dalar Amurka biliyan 500.

Kakakin ya bayyana haka ne, a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin, inda ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son yin yakin cinikayya, amma kuma ba ta jin tsoron sa, tana ma tsayawa kan matsayinta na yin yakin cinikayya ala tilas idan akwai bukatar hakan.

A Juma'ar da ta gabata ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana wa manema labaru cewa, a shirye yake ya karbi haraji kan kayayyakin cinikayya daga kasar Sin, wanda yawansu zai kai dala biliyan 500. (Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China