in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar cinikin Sin ta gabatar da jawabi kan karar da Amurka ta kai ga WTO game da batun buga haraji
2018-07-19 10:33:21 cri

Wani jami'in ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ya gabatar da wani jawabi a jiya 18 ga wata kan karar da Amurka ta kai ga WTO game da martanin da Sin take mayarwa kan matakin da Amurka take dauka na kara buga haraji kan karafa da sanholo da za ta fitarwa Amurka bisa nazarin da Amurka ta yi mai lamba 232, inda ma'aikatar ta nuna cewa, matakin da Sin take dauka ya yi daidai kuma ya dace da ka'idojin yin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, ya kamata Amurka ta yi watsi da matakan da take dauka wanda ya sabawa dokar WTO.

An ba da labarin cewa, a ranar 16 ga wata, Amurka ta kai kara ga tsarin daidaita takardama na WTO, inda ta ce, matakin da Sin take dauka kan mataki na 232 da Amurka ke dauka game da karafa da sanholo ya sabawa ka'idojin WTO.

Jami'in ya ce, matakin da Amurka ke dauka yana lalata ka'idojin yin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, wanda ya kawo illa ga moriyar mambobin WTO ciki hadda kasar Sin. Sin ta riga ta mikawa Amurka rokon shawarwari bisa ka'idojin WTO, amma Amurka ta ki ba da amsa. Bisa dokar ciniki da kasashen waje ta kasar Sin, kasar ta Sin ta dauki matakin da ya dace don dakile illar da Amurka za ta haifar mata da kuma kiyaye moriyarta. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China