in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin jihohin Amurka da dama na yin kira da a kara hadin kai da kasar Sin
2018-07-22 15:35:21 cri
An gudanar da taron yanayin zafi na majalisar shugabannin jihohin Amurka daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Yuli a Santa Fe, babban birnin jihar New mexico. Shugabannin jihohi da dama sun bada muhimmanci sosai kan dangantakar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Amurka, tare kuma da yin kira da kara hadin kai a wadannan fannoni a nan gaba.

Shugaban jihar Colorado John Hickenlooper ya nuna cewa, zurfafa hadin kan Sin da Amurka zai bada gudunmawa ga raya dangantakar kasashen biyu yayin da suke fuskantar takaddama da mawuyancin hali a tsakaninsu. Jihar za ta ci gaba da kara hadin kai da kasar Sin da kara fahimtar juna da amincewa da juna.

Shugaban jihar Utah, Gary Herbert, shi ma ya bayyana a gun taron cewa, Amurka na bukatar shiga kasuwannin duniya, ya kamata kasar ta kara hadin kai da tuntubar juna da kasashen duniya a maimakon rufe kofarta.

Ban da wannan kuma, shugabannin jihohi daban-daban mahalartan taron sun bayyana ra'ayinsu na kara hadin kai da kasar Sin, a ganinsu takaddamar da Amurka ta tayar a fannin ciniki ta kawo illa ga kayayyakin gona da sauran kayyaki masu kyau da Amurka take fitarwa kasashen waje, har ma ta samar da rashin tabbas a fannin zuba jari da bunkasuwar wasu kamfanonin kasar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China