in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara gabatar da korafi gaban WTO da Sin take yi ya yi daidai
2018-07-20 10:37:37 cri

Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a jiya 19 ga wata cewa, Sin ta kara gabatar da korafin ta ga kungiyar cinikayya ta duniya WTO, game da matakin kara harajin dala biliyan 200 da Amurka ke shirin aiwatarwa kan hajojin kasar Sin, matakin da jami'in ya ce ya yi daidai, kuma ya dace da tushen ka'idar WTO.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Gao Feng ya nuna cewa, harajin dala biliyan 34 da Amurka ta sanyawa kasar Sin, ya sabawa ka'idar baiwa wasu kasashe gatanci, da nauyin kayyade haraji, hakan ya kuma sa Sin ta kai kara a gaban WTO.

A wannan karo dai Amurka ta yi shirin kakabawa kasar Sin karin haraji da yawan sa ya kai dala biliyan 200, Sin kuma ta riga ta kara kai kara. Gao Feng ya ce, ko shakka babu Sin za ta dauki matakin da ya dace don mayar da martini ala tilas, bisa matakin da Amurka ke dauka na tsananta takaddamar ciniki tsakaninsu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China