Warren Buffett ya ce, wani muhimmin dalilin da ya sa tattalin arzikin kasar Sin ya habaka shi ne, kara karfafa gwiwar jama'ar kasar da gwamnati ke yi wajen yin kirkire-kirkire. Mista Buffett yana ganin cewa, idan wata kasa na son samun ci gaba, to ya kamata ta koyi darasin kasar Sin na baiwa al'ummarta kwarin-gwiwar yin kirkire-kirkire. Ya kuma ce, al'ummar kasar Sin na da basirar da Allah ya huwace musu, a don haka, dole tattalin arzikin kasar ya fuskanci kyakkyawar makoma.
Har wa yau, Warren Buffett ya ce, kamfanoninsa za su habaka zuba jari a kasashe irin Sin, wadanda ke da kyakkyawar makomar tattalin arziki.(Murtala Zhang)