in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COMESA ta nada Chileshe Kapwepwe babbar sakatariya
2018-07-19 10:10:50 cri

Kungiyar kawancen kasuwanni ta gabashi da kudancin Afirka ko COMESA a takaice, ta bayyana nadin Chileshe Kapwepwe a matsayin sabuwar babbar sakatariyar kungiyar.

An tabbatar da nadin Chileshe Kapwepwe, wadda a baya ta taba kasancewa mataimakiyar minista a ma'aikatar kudi ta kasar Zambia tsakanin shekaru 2008 zuwa 2011 ne, yayin taro na 20 na shugabannin kasashe mambobin kungiyar, wanda ya gudana a birnin Lusaka, fadar mulkin kasar ta Zambia.

Kapwepwe za ta maye gurbin Sindiso Ngwenya 'dan asalin kasar Zimbabwe wanda ya yi murabus, za kuma ta zamo mace ta farko da za ta rike wannan mukami a kungiyar kasuwanci mafi girma a shiyyar gabashi da kudancin nahiyar Afirka.

Kapwepwe, wadda ke da kwarewa a fannin aikin akanta, ita ce kuma shugabar hukumar tattara haraji ta kasar Zambia, ta taba zama kuma shugabar karba karba ta asusun ba da lamuni na IMF sashen nahiyar Afirka na daya a shekarar 2012.

An kafa kungiyar COMESA mai mambobi 21 ne a watan Disambar shekarar 1994, domin maye gurbin yankin hada hadar cinikayya da ya taba kasancewa a sashen a shekarar 1981, bayan da aka amince da shigar da kasashen Tunisia da Somalia.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China