in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU da COMESA sun rattaba hannu kan yarjejeniyar bunkasa cinikayya
2017-06-01 10:38:33 cri

Tarrayar Turai EU ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta shafi harkokin kudi da kungiyar cinikayya mafi girma a Afrika COMESA, domin inganta hadin kai ta fannin cinikayya.

Wakilin EU a Zambia da kungiyar COMESA Alessandro Mariani shi ne ya sanya hannu a kan yarjejejiyar a madadin EU, yayin da sakatare janar na kungiyar raya tattalin arzikin yankunan gabashi da kudancin Afrika COMESA Sindiso Ngwenya ya rattaba a madadin kungiyar.

Yarjejeniyar da aka cimma a jiya, ta kunshi jimilar Euro miliyan 68 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 76, da za a yi amfani da su domin aiwatar da shirye-shirye dake da nufin rage tsadar gudanar da kasuwanci tsakanin kasashe mambobin COMESA.

A cewar yarjejeniyar, shirin na saukaka matakan cinikayya na da nufin rage tsadar gudanar da kasuwanci da kuma safarar kayayyaki a yankunan kungiyar, inda za ta tallafawa wasu muhimman bangarori biyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China