Rasha: Amurka ta ci gaba da kera makamai masu linzami da yarjejeniyar IRBM ta haramta
Direktan cibiyar rage hadarin makaman nukiliya ta ma'aikatar tsaron kasar Rasha Sergey Ryzhikov ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Amurka tana ci gaba da kera makamai masu linzami da aka haramta a cikin yarjejeniyar soke makamai masu linzami masu cin matsakaici da gajeren zango da tsohuwar tarayyar Soviet da kasar Amurka wato IRBM suka aka daddale a ranar 8 ga watan Disamba na shekarar 1987. A shekarun baya baya nan, kasashen Amurka da Rasha sun sha zargin juna da sabawa wannan yarjejeniya. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku