in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kara shigar da kara a gaban WTO game da karin harajin da Amurka ta sanya kan kayayyakin da Sin za ta fitar zuwa kasar
2018-07-16 17:23:11 cri

Shafin intanet na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta kara shigar da kara a gaban hukumar WTO game da karin harajin da Amurka ta sanya kan kayayyakin da kasar Sin za ta fitar da su zuwa kasar wadanda darajarsu ta kai dala biliyan dari biyu.

A ranar 11 ga wannan wata ne kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya yi jawabi game da wannan batu, inda ya ce kasar Sin ba ta amince da matakin da Amurka ke dauka ba.

Kana a yayin taron manema labaru da aka gudanar a ranar 12 ga wannan wata, kakakin ya jaddada cewa, Sin ba za ta amince da ra'ayin kama karya kan ciniki na kasar Amurka ba, kuma za ta mayar da martani don kare muradunta da na jama'arta tare da tsarin yin ciniki cikin 'yanci na duniya da tsarin kasancewar bangarori daban daban. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China