in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sanarwar ma'aikatar kasuwancin kasar Sin dangane da manufar karbar karin harajin kwastam ta Amurka
2018-07-13 10:30:12 cri
Bayan ofishin wakilin ciniki na Amurka ya sanar da wani bayani dangane da "bincike mai lamba 301" da kasar take yi, a ranar 10 ga wata, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta mayar da martani, inda ta sanar da cewa:

Na farko, zargin da Amurka ke wa kasar Sin na daukar mataki maras adalci cikin cinikin da ake yi don neman riba, ba shi da tushe. Inda ta ce hakika Amurka ta na kokarin shafawa kasar Sin kashin kaza ne, da nufin tabbatar da muradunta a fannin siyasa, da yunkurin hana kasar Sin samun ci gaba.

Na biyu, ta musanta zargin da Amurka ta yi cewa kasar Sin ta yi fatali da sabanin ra'ayin da ake samu tsakanin Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya. Tana mai cewa, kasar Sin tana daukar sabanin ra'ayin da ake da shi da muhimmanci, kuma tana kokarin neman daidaita lamarin ta hanyar shawarwari.

Na uku, Amurka ta ce matakin da kasar Sin ta dauka don mayar da martani ga manufar Amurka ya keta doka. Amma a hakika abin da ya saba wa dokokin kasa da kasa shi ne yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar bisa radin kanta.

Na hudu, kasar Sin ta dauki matakin ne don kare muradun kasa da tattalin arzikin duniya, don haka matakin halaltacce ne kuma mai adalci.

Na biyar, bisa yakin cinikin da ta tayar, kasar Amurka tana mai da al'ummun duniya abokan gabanta, inda take haifar da barazana ga tattalin arzikin duniya.

Na shida, duk da matsin lambar da ake mata, kasar Sin za ta tsaya kan manufarta ta "bude kofa ga kasashen waje da gyare-gyare a gida", gami da kokarin kare manufar ciniki cikin 'yanci da tsarin ciniki da bangarori daban daban suka tsara tare. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China