in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude sabon ofishin jakadancin Amurka dake Isra'ila
2018-05-15 11:01:42 cri

A jiya ne, aka bude sabon ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Isra'ila a birnin Kudus, inda Palesdinawa da wasu kasashe da dama suka yi Allah wadai da wannan batu. A wannan rana, Palesdinawa sun yi zanga-zanga a wurare daban daban na kasar Palesdinu, inda suka arangama da sojojin Isra'ila, lamarin da ya haddasa mutuwar Palesdinawa 55, baya ga mutane fiye da 2800 da suka jikkata.

Mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Sullivan ne ya jagoranci tawagar wakilan kasar Amurka a bikin bude sabon ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar ta Isra'ila, ciki har da 'yar shugaban kasar Amurka Donald Trump Ivanka Trump da mai gidanta Jared Kushner da sakataren kudi na kasar Steven Terner Mnuchin.

Palesdinawa dai sun yi zanga-zanga a tsakanin zirin Gaza da kasar Isra'ila da biranen Ramallah, Bethlehem, Hebron, Jerico da sauransu, inda suka yi taho mu gama da sojojin kasar Isra'ila, wanda ya haddasa mutuwar Palesdinawa 55, tare da raunatar mutane fiye da 2800.

Kafofin watsa labaru na kasar Isra'ila sun sanar da cewa, yawan Palesdinawan da suka mutu a yini guda shi ne adadi mafi yawa tun bayan da aka fara yakin zirin Gaza a shekarar 2014.

A wannan rana, jami'an gwamnatocin kasashen Faransa da Lebanon da Jordan da Masar da kungiyar kasashen Larabawa sun bayar da sanarwa, inda suka yi Allah wadai da nuna rashin amincewa da matakin kasar Amurka na dawo da ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Kudus, tare da yin kira ga mahukuntan kasar Isra'ila da su kai zuciya nesa wajen yin amfani da karfin tuwo. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China