in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta sake 'yan matan makarantar Dapchi 104
2018-03-22 09:07:45 cri

A jiya Laraba ne aka sako 'yan mata 104 na sakataren kimiyya da fasaha ta Dapchi dake jihar Yobe a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya wadanda kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ta sace a watan jiya.

Ministan yada labarai da raya al'adu na Najeriyar Lai Mohammed, ya bayyana cewa, an sako wani yaro guda da kuma wata karamar yarinya tare da 'yan matan makarantar 104.

Mohammed ya ce, an sako dukkan mutanen 106 ne ba tare da gindaya wani sharadi ba, kuma ba'a biya kudin fansa ba, ko kuma yin musayar fursunoni da mayakan na Boko Haram gabanin su amince da sakin 'yan matan.

Ministan ya tabbatar da cewa, tuni dakarun sojin Najeriyar suka mika yaran da aka kubutar ga hannun gwamnati a hukumance. An gudanar da mika yaran ga gwamnatin ne a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar.

Tuni dai aka kwashe 'yan matan makarantar su 104 tare da sauran yaran biyu da aka kubutar tun a jiya Laraba a cikin wani jirgin saman soji zuwa babban birnin tarayya Abuja.

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne aka yi garkuwa da 'yan matan su 110 a wata kwalejin kimiyya da fasaha ta 'yan mata dake garin Dapchi, mai tazarar kilomita 100 daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China