in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 149 da mayakan Boko Haram suke rike da su
2018-04-09 09:02:36 cri

A jiya Lahadi rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa, ta kubutar da mutane 149 wadanda mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su bayan da sojojin suka kaddamar da samame a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Dakarun sojin sun kuma hallaka 'yan ta'addan 5 a yayin arangama da mayakan a yankin Yerimari-Kura, dake kusa da dajin Sambisa, kanal Onyeama Nwachukwu, kakakin rundunar sojin Najeriya ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa.

Nwachukwu ya ce, wadanda aka bukutar sun hada mata 54 da kananan yara 95.

Kakakin rundunar ya kara da cewa, sojojin sun samu nasarar dakile yunkurin wasu 'yan kunar bakin wake su biyu wadanda suke shirin kaddamar da harin a unguwar Mandanari dake garin Konduga a jihar Borno a ranar 7 ga watan nan na Afrilu.

Dakarun Najeriya suna samun gagarumar nasara a yakin da suke da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram, inda suka yi nasarar fatattakar su daga babbar maboyarsu dake dajin Sambisa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China