in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 86 aka hallaka a shiyyar tsakiyar Najeriya
2018-06-25 09:23:01 cri

A kalla mutane 86 ne aka kashe a sanadiyyar wasu hare hare da aka kaddamar a wasu kauyuka masu yawa a jihar Plateau dake shiryyar tsakiyar Najeriya, kamar yadda hukumar 'yan sanda ta sanar a jiya Lahadi.

Hare haren wadanda ake zargin wasu 'yan bindiga da kaddamarwa da yammacin ranar Asabar ya jikkata mutane 6 da kona gidaje 50, da motoci biyu, da babura 15, in ji hukumar 'yan sandan.

Kakakin hukumar 'yan sandan ya ce, kawo yanzu ba'a gano dalilin kai harin ba.

Hare haren ya shafi kauyukan Razat, Ruku, Nyarr, Kura da Gana-Ropp dake gundumar Gashish a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Plateau, in ji Terna Tyopev, kakakin hukumar 'yan sandan jihar Plateau.

Kimanin kauyuka 11 ne 'yan bindigar suka kaddamar da hare haren.

Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dokar takaita zirga zirga a yankunan da rikicin ya shafa sakamakon fargabar sake barkewar tashin hankalin.

Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong, wanda ya bayyana harin a matsayin abin tada hankali ya bukaci hukumomin tsaro da su ninka kokarin da suke yi domin kawo karshen hare haren dake faruwa a yankunan karkara na jihar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China