in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin ta bayyana yakin cinikayya a matsayin yaki tsakanin fin karfi da ka'ida
2018-07-11 19:13:46 cri

A jiya Talata ne ofishin wakilin cinikayya na kasar Amurka, ya sanar da aniyar kasar ta kara kudaden haraji har kaso 10 bisa dari, a kan jerin kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa Amurka, wadanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 200. A yau kuma Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta jaddada a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, matakin da kasar Amurka ta dauka, makarkashiyar nuna fin karfi ne a fannin cinikayya.

Jami'ar ta kara da cewa, kasar Sin za ta mayar da martani na wajibi, domin kare hakki da moriyar halal ta ta, kuma a bayyane take cewa, yakin cinikayya yaki ne tsakanin cinikayyar kashin kai, da cinikayya tsakanin bangarori da dama, da ba da kariya ga cinikayya, da cinikayya maras shinge. Haka kuma yaki ne dake tsakanin fin karfi da ka'ida.

Har ila yau kasar Sin tana son sanya kokari tare da sauran kasashen duniya, domin kiyaye tsari da ka'idar cinikayya tsakanin bangarori da dama. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China