in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wanda bai nuna kiyayya ga yakin cinikayya ba zai gamu da matsala
2018-07-09 19:11:16 cri

Tun daga farkon watan Yulin da muke ciki, kasashen duniya da dama sun nuna kiyayya ga yakin cinikayyar da gwamnatin Trump ta kaddamar, misali kasar Canada ta kara kudaden haraji a kan jerin kayayyakin da kasar ke shigarwa kasar Amurka, wanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 12 da miliyan 600, kana kasar Mexico ta sake kara kudaden haraji a kan jerin kayayyakin da take shigarwa Amurka, wadanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 3 a karo na biyu.

Ya zuwa ranar 6 ga wata, kasar Sin ita ma ta ga tilas ta kara kudaden haraji a kan jerin kayayyakin da kasar ke shigarwa kasar Amurka, wanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 34. A kuma wannan rana, kasar Rasha ita ma ta sanar da cewa, za ta kara kudaden haraji a kan wasu kayayyakin da kasar ke shigarwa kasar Amurka.

A cikin wannan yakin cinikayya dake da nasaba da moriyar daukacin kasashen duniya, an yi hasashen cewa, kasashe da dama za su ga wajibcin daukar wajibabbun matakai. A karkashin irin wannan yanayi, wasu kasashe wadanda ba su nuna kiyayya ga yakin ba, za su gamu da matsala.

Da farko dai, kada a manta da wadda ke tayar da yakin cinikayyar. Kila ne za a manta da Amurka, ita ce kasa wadda ke tayar da wannan yaki na cinikayya, a don haka kasashen Canada da Mexico da kuma kasar Sin suka dauki matakai domin mayar da martini.

A bayyane ne ana iya fahimtar cewa, idan ana son kawo karshen yakin cinikayyar, dole ne Amurka canja tunaninsa, haka kuma ta daina yin yakin cinikayya.

Na biyu, bai kamata wata kasa ta yi zaton cewa, yakin cinikayyar ba shi da nasaba da ita ba, dole ne ko wace kasa ta dauki matakin da ya dace, domin mayar da martani. A ranar 7 ga wata, tashar yanar gizo ta kasar Japan ta "Nikkei Asian Review" ta bayar da wani sharhi, inda aka bayyana cewa, ya kamata a koyi darasi daga tarihin yakin cinikayya na tsohon shugaban kasar Amurka Herbert Clark Hoover a shekarar 1930, a wancan lokaci, domin ba da kariya ga masana'antun kasarsa, shugaba Hoover ya sa niyyar kara kudaden haraji a kan kayayyakin da kasar take shigowa da su daga kasashen waje, duk da cewa masanan tattalin arzikin kasar sama da dubu daya sun nuna kiyayyar su da matakin. A sakamakon haka, kasashen Turai suka dauki matakai domin mayar da martani, a karshen dai, yakin cinikayyar ya jefa tattalin arzikin duniya a wancan lokaci cikin mawuyacin hali.

Na uku, ya dace a dauki matakai tare, bai kamata ba wata kasa ta dauki mataki bisa radin kanta ita kadai. Yanzu haka kasar Amurka ta tayar da yakin cinikayya, don haka ya dace sauran kasashen duniya su dauki matakai tare domin mayar da martani.

Bisa matsayinta na babbar kasa a duniya, kasar Sin tana daukar matakai mafiya karfi, kasar tana kuma fatan sauran kasashen duniya za su yi kokari tare da ita, duba da cewa mai yiwuwa wanda ma bai nuna kiyayya ga yakin cinikayyar ba shi ma matsalar ta shafe shi.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China