in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar kasuwancin Sin ya yi bayani kan manufar sassauta rigingimun cinikayya
2018-07-09 20:30:00 cri

A yau Litinin ne kakakin ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, yayin da kasar Sin take yin nazari kan jerin kayayyakin kasar Amurka da za ta karawa kudaden haraji, ta riga ta yi la'akari sosai, haka kuma ta yi la'akari kan tasirin da hakan zai kawo ga muhallin zuba jari a kasar ta Sin. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai guda hudu kan batun:

Na farko, za ta ci gaba da tantance tasirin da hakan zai kawo wa kamfanonin kasar. Na biyu, za a yi amfani da kudin shigar da za a samu daga kudaden harajin da za a kara, a aikin sassauta matsalolin da kamfanoni da ma'aikatansu suke fuskantar. Na uku, za a sa kaimi kan kamfanonin, ta yadda za su kyautata tsarin shigo da kayayyaki daga ketare, wato su kara shigo da wake da kayan aikin gona, da abincin ruwa, da mota daga sauran kasashe. Na hudu, za a kara kokarin aiwatar da manufar da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar a ranar 15 ga watan Yunin bana, game da yin amfani da jarin waje da kyautata ingancin tattalin arziki, tare kuma da kare hakkin halal na kamfanonin, ta yadda za a kara kyautata muhalin zuba jari a kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China