in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga gwamnatocin Afrika da su samar da kudaden bunkasa bangaren ilimi
2018-04-27 10:10:34 cri
Masu rajin kare ilimi, sun bukaci gwamnatocin nahiyar Afrika, su samar da tsarin samar da kudade da zai taimaka wajen fadada damar samun ilimi ga marasa galihu da matasa.

Masu rajin, sun bayyana haka ne yayin taron nahiyar kan ilimi dake gudana a birnin Nairobin Kenya.

Wani babban jami'i a Kungiyar raya ilimi a Afrika Makha Ndao, ya ce wajibi ne a yi amfani da sabon tsarin na samar da kudaden don taimakawa shirye-shiryen inganta ilimi da fasahohi a Afrika.

Ya ce ya kamata a mayar da hankali ga samar da kudi ga bangaren ilimi a nahiyar, la'akari da yadda tallafin da ake samu daga al'ummomin kasashen waje ke raguwa.

A cewar MDD, nahiyar Afrika na bukatar karin dala biliyan 40 domin cimma muradi na 4, dake cikin muradun ci gaba masu dorewa kan ilimi, ya zuwa 2030.

Masu rajin sun kuma bukaci gwamnatocin Afrika su maganace duk wasu manufofi dake tarnaki ga samar da isasshen kudi ga bangaren ilimi. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China