in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matasan Afrika na da muhimmanci wajen raya tattalin arzikin nahiyar
2018-04-29 15:52:46 cri
Mataimakin sakataren zartarwa na hukumar kula da tattalin azriki ta MDD Abdalla Hamdok, ya ce burin matasan Afrika, shi ne babban albarkar da fata mafi kyau na karfafa ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Da yake zantawa da Xinhua a gefen taron karshen mako na shekara-shekara kan muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar Afrika na gidauniyar Mo Ibrahim, Abdalla Hamdok ya ce matasa 'yan kasa da shekaru 25 ne suka mamaye kaso 60 na al'ummar nahiyar, kuma kawo shekarar 2050, nahiyar za ta dauki mutane miliyan 452 'yan kasa da shekaru 25.

Ya ce karfin wadanan matasa da burinsu da abubuwan da za su iya zai ba kasashen Afrika kadarar da ba sa taba gani ba.

Abdalla Hamdok wanda kuma shi ne shugaban majalisar bada shawara ta gidauniyar, ya ce galibin matasan Afrika na shafe shekaru da dama a makaranta, amma kuma ba sa samun fasahohin da suka kamata, wanda ci gaban tattalin arziki ke bukata, abun da ke barazana ga bunkasar nahiyar.

Ya kuma yi kira ga dukkanin kasashen Afrika su samarwa da matasa ilimi da fasahohin da suka dace, domin ba su damar kai wa ga cimma ajandar nahiyar ta sauya fasalin tattalin arziki.

A cewar wani rahoton nazarin tattalin arziki na bankin raya Afrika, ya ce ana sa ran karuwar al'ummar Afrika zai kara yawan kudin da ake kashewa na sayen kayayyakin amfani daga dala biliyan 680 a 2008 zuwa dala triliyan 2.2 a shekarar 2030. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China