in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen shiyyar gabashin Afrika sun bukaci hada kai don cigaban yankin kogin Nilu
2018-02-23 10:50:27 cri
Kasashen yankin gabashin Afrika wadan da suka hallara a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, domin bikin murnar ranar kogin Nilu, sun bukaci yin aiki tare da daukar matakan da zasu tabbatar da cigaban kogi na Nilu.

An gudanar da bikin na ranar kogin Nilu ne mai taken: "Hadin gwiwa game da batun kogi, aikine na bai daya," kungiyar mambobin kasashen kogin Nilu (NBI), sun nanata aniyar burin da suke dashi na yin amfani da kogi mafi girma a duniya don cin moriyarsa.

Da yake jawabi a lokacin bikin ranar kogin Nilun karo na 12, babban daraktan NBI, Innocent Ntabana, ya bukaci a hada karfi da karfe don yin hadin gwiwa a tsakanin mambobin kasashen domin cin moriyar kogin da ba shi kariyar da ta dace.

Ntabana yace, domin cimma nasarar amfana daga dunbun albarkatun dake tattare da kogin, ya zama tilas gamayyar kasashen dake da nasaba da kogin su yi aiki tare, domin kare martabar kogin da kiyaye shi don biyan muradun kasashen da lamarin ya shafa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China